Isa ga babban shafi

Inter Miami za ta doka wasan karshe na cin kofin US Open ba tare da Messi ba

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami Gerardo Martino ya ce za su dauki kasadar doka wasan karshe na cin kofin US Open ba tare da tauraronsu Lionel Messi ba, wanda rauni zai hana shi doka wasan a tsakaninsu da Houston Dynamo a gobe Alhamis.  

Messi na Argentina da ke taka leda da Inter Miami.
Messi na Argentina da ke taka leda da Inter Miami. AP - Eduardo Munoz Alvarez
Talla

A minti na 37 da fara wasa ne tsakanin Inter Miami da Orlando City aka cire Messi daga wasan saboda raunin da ya samu dalilin da zai hana shi samun damar taka leda a karawar ta gobe Alhamis wanda kungiyar ke fatan lashe kofin na US Open.

A cewar Martino, Messi ya yi fami ne akan tsohon raunin da ya samu tun kafin ya zo kungiyar amma sun yi tsammanin ya iya warwarewa kafin wasan na karshe a gobe, amma kuma alamu na nuna da wuyar ya iya taka leda a wasan.

Messi wanda Inter Miami ta sayo daga PSG cikin watan Yulin da ya gabata, zuwa yanzu ya zura kwallaye 11 a wasanni 12.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.