Isa ga babban shafi
DAMBEN GARGAJIYA

An kammala shirye-shiryen gudanar da wasan karshe na dambe a Kano

Cibiyar dake shirya gasar wasan Dambe ta Najeriya wato Dambe Warriors Suoerfight ta ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da wasan karshe na gasar a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.

Wasu 'yan dambe a Kano, Najeriya.
Wasu 'yan dambe a Kano, Najeriya. © dambe warriors
Talla

Jagoran masu shirya gasar Mr Aminu Bature Kucheri ya ce a yanzu gasar ta zama ta kasa har ma da wajen Najeriya, kasancewar akwai dan asalin kasar Saudiyya da zai fafata a wasan karshen da za gudanar ranar 26 ga watan Nuwamban da muke ciki.

Wasan dambe da ya samo asali daga kasar Hausa na ci gaba da daukar hankalin Jama'a daga ciki da wajen Najeriya, inda ake shirya gasar wasan yanzu a zamanance.

Za a fafata wasan ne a rukuni uku da suka hada da ajin kanana da matsakaita da kuma ajin masu nauyi ciki har da dan kasar Saudiyya Hussain, inda za su kara da Cisco na Najeriya a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano

Gasar ta Dambe Warriors Suoerfight, ana shirya ta ne duk shekardomin zakulo sababbin 'yan wasa da za su ci gaba da daga martabar wasan a idon duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.