Isa ga babban shafi

Karon farko cikin shekaru 24 dan Najeriya ya shiga sahun manyan 'yan kwallon duniya

A karon farko cikin shekaru 24, dan wasan gaba na tawagar Najeriya Victor Osimhen ya shiga cikin jeren ‘yan wasan da suka yi takarar lashe kyautar Ballon d’Or da aka bayar a jiya Litinin.

Dan wasan Najeriya da Napoli Victor Osimhen.
Dan wasan Najeriya da Napoli Victor Osimhen. REUTERS - JENNIFER LORENZINI
Talla

Dan wasan dai ya kare ne a mataki na 8, gaban manyan ‘yan wasa irinsu Karim Benzema da Jude Bellingham da Robert Lewandowski da kuma Mohamed Salah.

Rabon da wani dan wasan Najeriya ya shiga wannan takara tun shekarar 1999, lokacin Nwankwo Kanu, tsohon kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeriya.

 Tsohon kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeirya Nwankwo Kanu.
Tsohon kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeirya Nwankwo Kanu. Reuters

Osimhen mai shekaru 24 ya kafa tarihin zama dan wasan Afrika na farko da ya lashe kofin gasar Serie A da kuma takalmin zinari na gasar a kaka dara, bayan da ya jefa wa kungiyarsa ta Napoli kwallaye 26 a gasar Serie A, sannan ya ci mata kwallaye 31 a wasanni 39 da ya buga mata a dukkanin gasanni.

Haka nan dan wasan ya taimakawa tawagar kasarsa ta Super Eagles wajen samun gurbin zuwa gasar lashe kofin Afrika, inda ya zura kwallaye 10 a raga a wasannin neman gurbin shiga, lamarin da ya bashi damar karewa a mataki na farko na yawan kwallaye a wasannin .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.