Isa ga babban shafi

An soke kwantiragin El Ghazi saboda sakon goyon bayan Falasdinu

Tsohon dan wasan Aston Villa da Everton Anwar El Ghazi ya rasa kwantiraginsa a Mainz saboda wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta game da rikicin Isra'ila da Gaza.

Dan wasan Holland Anwar El Ghazi yayin taka leda a Lille a 2017
Dan wasan Holland Anwar El Ghazi yayin taka leda a Lille a 2017 AFP
Talla

Tun a ranar 17 ga watan nan, Kulob din dake taka leda a Bundesliga ya dakatar da El Ghazi, wanda ya kira sakon da tuni aka shere da cewa ba abin lamunta ba ne.

A wata ganawa da suka yi a ranar Alhamis, kulob din ya bukaci dan wasan mai shekaru 28 da ya nemi afuwa kan rubutun da ke zama goyon bayan Falasdinu.

Amma dan kasar Holland din ya shaida wa manyan jami'an club din cewa yana fifata zaman lafiya da kuma jinkai ga duk wadanda yakin Gaza ya shafa, abin da ya sa majiyoyi suka ce klub din ya sanar da shirin soke kwantiragin El Ghazi.

Ya koma klub din daga PSV

A ranar 22 ga watan Satumba ya koma kungiyar kyauta a bayan ya bar PSV Eindhoven.

A karkashin dokar kwadago ta Jamus, wa’adin kwanaki 14 ake iya korar ma’aikaci daga ranar da aka fahimci rashin da’a, sabanin haka dole ne sai an biya kudin cinikin baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.