Benzema na da 'yancin nuna jimami kan halin da Falasdinawa ke ciki - Lauyansa
Lauyan Karim Benzema ya mayar da martani ga ministan cikin gidan Faransa bayan da ya zargi tauraron kwallon kafar Faransa da alaka da kungiyar 'yan uwa musulmi.
Wallafawa ranar:
Ministan harkokin cikin gida Gerald Darmanin ne ya yi wannan zargin bayan dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d’Or kuma tsohon dan wasan gaba na Real Madrid ya wallafa wani sako a shafukan sada zumunta game da goyan bayan Falasdinu a yakin da ake yi tsakanin Isra’ila da Hamas.
Benzema wanda ke taka leda a kungiyar Al Ittihad ta kasar Saudiyya, ya wallafa sakon goyan baya ga Falasdinawa ne ta shafinsa na X.
"Dukkan addu'o'inmu ga mazauna Gaza ne wadanda suka sake fuskantar wadannan hare-haren bama-bamai na rashin adalci, wanda bai ware mata da kananan yara ba."
Darmanin, da yake magana a tashar CNews, ya yi zargin cewa Benzema na da alaka da kungiyar 'yan uwa musulmi".
“Wannan karya ne! Karim Benzema bai taba samun wata dangantaka da wannan kungiyar ba,”in ji Hugues Vigier Lauyan Benzema a cikin wata sanarwa.
Ya ce Benzema kamar da dama daga al’ummar duniya na tausawa Faladinawa ne kan halin da suke ciki, wanda ake alakantawa da laifukan yaki a yankin Gaza, tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai cikin Isra’ila.
Lauyan ya kara da cewa yana shirin shigar da karar Darmanin kan zargin nasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu