Isa ga babban shafi

Bowen ya rattaba hannu a kwantragin shekaru bakwai da West Ham

Jarrod Bowen ya rattaba hannu kan sabon kwantragin shekaru bakwai da West Ham. Dan wasan mai shekaru 26, ya zura kwallaye 45 a wasanni 166 da ya buga wa Hammers, ciki har da wanda ya yi nasara a wasan karshe na gasar cin kofin Europa da aka buga a bara, inda ya lashe kyautar azurfa ta farko da kulob din ya samu tun 1980.

Dan wasan West Ham's Jarrod Bowen
Dan wasan West Ham's Jarrod Bowen POOL/AFP
Talla

Jarrod Bowen, wanda aka tuno da shi a tawagar Ingila a makon da ya gabata, ya zura kwallo biyar a wasanni tara a  kakar wasa ta bana.

Dan wasa Jarrod Bowen
Dan wasa Jarrod Bowen POOL/AFP

 

Dan wasan cikin rafin ciki y ana mai cewa "kowa ya san abin da West Ham ke nufi a gare ni, don haka sadaukar da rayuwata zuwa 2030 yana da matukar muhimmanci a gare ni da iyalina,".

Kocin West Ham David Moyes ya yaba da yarjejeniyar a matsayin wani babban labari ga kungiyar. Moyes ya ce "Burinsa a Prague zai dade cikin tunawa ga duk wanda ke da alaka da West Ham."

 

Yan Wasan West Ham
Yan Wasan West Ham © Ian Walton/AP

 

 

Bowen, wanda ya koma West Ham daga Hull kan fan miliyan 18 a shekarar 2020, a baya ana alakanta shi da komawa Liverpool a matsayin wanda zai maye gurbin Mohamed Salah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.