Isa ga babban shafi
WASANNI-FC NANTES-CARDIFF CITY

Kungiyoyin kwallon kafar, Cardiff City, ta Ingila da FC Nantes, ta Faransa sun karata a kotu.

A jiya alhamis ne Kungiyoyin kwallon kafar Cardiff City da FC Nantes,   suka gurfana a gaban kotu Faransa, inda kungiyar ta kasar Birtaniya ke bukatar  biyata diyar euro miliyan 100,  bayan mutuwar dan wasanta joueur Emiliano Sala a 2019 ta hanyar hatsari.Dan wasan dan lkasar Arjentina Emiliano Sala, mai shekaru 28 a duniya ya mutu ne a watan janairun 2019,  a sanadiyar wani hatsarin jirgin sama kan hanyarsa ta sabon club din da ya saye shi daga FC Nantes, wato Cardiff City.

Lors d'un hommage au footballeur Emiliano Sala.
Lors d'un hommage au footballeur Emiliano Sala. AFP
Talla

Club din "Cardiff dai ya kaddamar da gagarumar rigima da FC Nantes,  tun bayan hadarin da ya yi sanadiyar rasa ran Emiliano Sala, da  hakan ya kai su  kotu, kamar yadda  daya daga cikin lauyoyin kungiyar kwallon kafar ta Faransa FC Nantes.

Idan dai ba a manta ba komitin dake kula da tsara dokokin yan wasa na hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ya sa kafar wando guda da kungiyar  Nante, kafin ya cimma rashin nasara a gaban kotun warware rikice rikicen wasanin motsa jiki ta duniya, TAS a kasar Suisse.

Lauyoyin dai sun ce, kungiyar ta Cardiff,  ba ta kammala biyan  FC Nantes gabadayan kudaden alawus din saida dan wasan  da suka kai Euro miliyan 17 ba.

A cewar lauyoyin kungiyar ta Cardif, ta karbi kashin farko na Euro miliyan shidda ne kacal daga  kudaden alawus din marigayin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.