Isa ga babban shafi

Bordeaux ta fusata da hukuncin hukumar kwallon kafar Faransa

Hukuncin hukumar kwallon kafar Faransa na bai wa Bordeaux rashin nasara a wasansu da Rodez da aka dakatar ya hana kungiyar samun damar tsallakewa daga gasar Lig 2.

Filin wasa na Bordeaux.
Filin wasa na Bordeaux. FRANCK FIFE / AFP
Talla

Yayin wasa tsakanin kungiyoyin biyu ne a ranar 2 ga watan Yuni wani magoyi baya da ya kutso cikin fili ya hankade Lucas Buades na Rodez dalilin da ya tilasta dakatar da wasan.

Wannan dalili ne ya sanya baiwa Bordeaux rashin nasara a karawar Wanda ke nuna cewa ta kammala gasar a matsayin ta 2 yayinda ita kuma Rodez ta tsallake rukunin ‘yan dagaaji na teburin gasar ta Lig 2, ta biyu mafi girma a Faransa.

Tuni dai Bordeaux ta fusata da wannan hukuncin inda ta sha alwashin daukaka kara ga kwamitin koli na harkokin wasanni a kasar don bi mata hakki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.