Isa ga babban shafi

Mbembe ya lashe kyautar Marc-Vivien Foe ta RFI/France24

Mai tsaron baya na Marseille Chancel Mbembe ya lashe kyautar gwarzon shekara ta Marc-Vivien Foe da gidan Radiyon RFI ke bayarwa ga zakakuran nahiyar Afrika da ke taka leda a karkashin gasar Lig 1.

Mai tsaron baya na Marseille da ya lashe kyautar Marc-Vivien Foé Chancel Mbemba, kyautar da RFI da FRANCE 24 ke bayarwa duk shekara.
Mai tsaron baya na Marseille da ya lashe kyautar Marc-Vivien Foé Chancel Mbemba, kyautar da RFI da FRANCE 24 ke bayarwa duk shekara. © RFI
Talla

Mbemba dan Congo mai shekaru 28 ya lashe kyautar ta bana ne bayan bajintar da ya nuna a kungiyarsa ta Marseille wadda ta kammala kakar bana a matsayin ta 3 a teburin gasar Lig 1, wanda ya bashi damar shiga gaban Seko Fofana dan Cote d’Ivoire da ya lashe kyautar a bara da kuma Terem Moffi na Najeriya.

'Yan wasan Afrika 3 da suka fafata wajen lashe kyautar ta Marc-Vivien Foe da suka kunshi Seko Fofana da Chancel Mbemba da kuma Terem Moffi.
'Yan wasan Afrika 3 da suka fafata wajen lashe kyautar ta Marc-Vivien Foe da suka kunshi Seko Fofana da Chancel Mbemba da kuma Terem Moffi. © Studio graphique FMM

Kyautar ta Marc-Vivien Foe da RFI ta fara bayarwa a shekarar 2009 na da nufin karrama dan wasan Kamaru Marc-Vivien da ya mutu lokacin da ya ke tsaka da dokawa kasar shi wasa tsakaninsu da Colombia a birnin Lyon na Faransa cikin watan Yunin shekarar 2003 ya na da shekaru 28.

Mbemba ya taka rawar gani a basarar Marseille cikin wannan kaka, kungiyar da za a ga haskawarta a gasar cin kofin zakarun Turai cikin shekara mai zuwa, bayan kammala wasannin gasar ta Lig 1 a sahun ‘yan hudun saman teburi.

Dan wasan na Congo Chancel Mbembe shi ne mai tsaron baya na farko da ya taba lashe wannan kyauta tun bayan fara bayar da ita shekaru 14 da suka gabata.

Haka zalika Mbemba ya zama dan wasa na biyu daga kasar Congo da ya lashe kyautar ta gwarzon shekara wadda ‘yan jaridun RFI da France 24 baya ga kwararru da ke sanya idanu kan wasanni da kuma tsaffin ‘yan kwallo ke tantancewa gabanin bayar da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.