Isa ga babban shafi

Messi zai bar PSG a karshen wannan kaka

Lionel Messi zai bar Paris St-Germain yayin da kwantiraginsa na yanzu zai kare a karshen wannan kaka.

Dan wasan gaban Argentina da PSG Lionel Messi.
Dan wasan gaban Argentina da PSG Lionel Messi. REUTERS - CHRISTIAN HARTMANN
Talla

Dan wasan wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a Argentina ya cimma ‘yarjejeniya bisa manufa’ na tsawaita zamansa na tsawon shekara guda amma babu batun sabunta yarjejeniyar.

Messi bai gamsu da cewa kungiyar za ta iya shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ba, saboda matsalar kudi, yayin da zakarun na Faransa ke son mayar da hankali wajen daukar matasan 'yan wasa.

Ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu a birnin Paris a shekarar 2021 tare da zabin sabunta yarjejeniyar shekara amma yanzu ba za a kunna shi ba.

Dan wasan ya yi imanin cewa za a iya iyakance kasafin kudin PSG a kakar wasa mai zuwa don bin ka'idojin dokar da ta kayyadewa kungiyoyi kashe kudade.

PSG ta dakatar da dan wasan mai shekaru 35 na tsawon makwanni biyu a ranar Talata bayan ya tafi Saudiyya ba tare da izinin kungiyar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.