Isa ga babban shafi

Tottenham ta kori cocinta Stellini bayan doke su da Newcastle ta yi da 6 - 1

Tottenham ta kori kocin rikon kwarya ta Cristian Stellini bayan da shugaban kungiyar Daniel Levy ya bayyana rashin amincewa da dukan kawo wuka da ta sha a hannun Newcastle da ci 6-1 a ranar Lahadi.

Kocin Tottenham na wucin gadi Cristian Stellini.23/04/23
Kocin Tottenham na wucin gadi Cristian Stellini.23/04/23 REUTERS - SCOTT HEPPELL
Talla

Stellini, wanda aka nada shi ne a watan jiya bayan tsohon mai gidansa Antonio Conte ya bar kungiyar, kuma tuni Ryan Mason ya maye gurbinsa nan ta ke.

Mataimakin Conte na dogon lokaci nasara daya kachal daga cikin wasanni hudu da ya jagoranta, ya haifar da cikas ga damar Spurs zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

Har yanzu Tottenham na matsayi na biyar a teburin Premier amma maki shida ne tsakaninta da ta hudu kuma da sauran akalla wasa daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.