Isa ga babban shafi

Richarlison ya musanta zargin hannu a korar da Tottenham ta yi wa Conte

Dan wasan gaba na Tottenham ya Richarlison ya musanta cewa ya taka rawa wajen tabbatar sallamar tsohon kocin kungiyar Antonio Conte, ya na mai cewa ya na matukar girmama tsohon mai horarwar. 

Dan wasan gaba na Tottenham.
Dan wasan gaba na Tottenham. © REUTERS/David Klein
Talla

Conte ya bar Tottenham mai doka gasar firimiyar Ingila ne a ranar Lahadin da ta gabata ta hanyar fahimtar juna, bayan da dangantaka tsakaninsa da mahukuntan kungiyar ta lalace a dukkanin matakai a ‘yan makonnin baya. 

Tsohon mai horar na Chelsea, Juventus da Inter Milan ya caccaki ‘yan wasansa bayan da suka buga canjarar 3-3 da Southampton gabanin hutun wasannin kasa da kasa, inda ya kira su da masu son kai, kalaman da ake ganin shi ya ja masa kora. 

Wasu rahotanni da suka bayyana sun nuna cewa Richarlison da dan wasan baya Cristian Romero sun bai wa kungiyar wa’adin wani lokaci kan ko dai ta sallami mai horarwar Antonio Conte, ko kuma su bar kungiyar, ko da ya ke tuni Richarlison, dan kasar Brazil ya musanta ikirarin a jiya Alhamis. 

A cewar Richarlison ba zai yiwu ya yi hakan ba, saboda Conte ya taimaka masa sosai a sana’arsa ta tamaula. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.