Isa ga babban shafi

Bayern ta dakatar da Mane saboda naushin da ya kirɓa wa Sane

Kungiyar Bayern Munich ta dakatar da dan wasanta Sadio Mane daga buga wasa daya, sakamakon naushin da ya kirba wa abokin wasansa Leroy Sane, bayan rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu.

Sadio Mané.
Sadio Mané. REUTERS - PHIL NOBLE
Talla

Wannan mataki dai na nufin Sadio Mane, mai shekaru 31, ba zai kasance cikin tawagar kungiyarsa da za ta fafata wasa da Hoffenheim ba a ranar Asabar mai zuwa.

Baya ga dakatarwar wasa guda Mane zai kuma biya tarar kudaden da a bayyana adadinsu ba.

Babu dai wanda zai iya tabbatar da hakikanin abinda ya haifar da takadddama tsakanin ‘yan wasan na Bayern Munich, illa wasu majiyoyi da suka ruaito cewar Mane ya zargi Leroy Sane da raina shi, abinda ya sa suka fara musayar yawu tun a cikin filin wasan da Manchester City  ta lallasa su da kwallaye 3-0 a ranar Talata.

Bayan shiga dakin hutu da adana kaya ne kuma lamarin ya kai ga bai wa hammata iska a tsakanin ‘yan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.