Isa ga babban shafi

Achraf Hakimi na shan yabo daga sassan duniya kan dabarar kare dukiyarsa

Rabuwar auren Hiba Abouk da Achraf Hakimi dan wasan Morocco, ya bazu a kafofin yada labarai,  bayan da aka ruwaito cewa matar ta shigar da kara kan dan wasan na Paris Saint-Germain da ya sake ta.

Dan wasan PSG da Morocco Achraf Hakimi kenan.
Dan wasan PSG da Morocco Achraf Hakimi kenan. PSG via Getty Images - Aurelien Meunier - PSG
Talla

Hakimi na fuskatar tuhuma bisa zargin yi wa wata mata fyade, lokacin da matarsa tare da yaransu da kuma mahaifiyarsa suka yi balagurio zuwa Dubai.

Mujallar First Mag ta Faransa ta ruwaito cewa Hiba na neman rabin kadarorin da Hakimi ya mallaka, amma ta yi mamaki da ta samu labarin cewa ba shi da komai a sunansa.

Hakan na nufin Abouk ba za ta karbi wani bangare na dukiyar tsohon mijin na ta ba

Wanda ke cin gajiyar albashi da dukiyar Hakimi ba kowa ba ne illa mahaifiyarsa wadda ta shafe shekaru da dama tana karbar albashin sa a asusun bankinta.

Duk da cewa wannan labari ya ya janyo hankali sosai a kasashen Spain Faransa da kuma Moroko, duk kuwa da cewa Abouk ba ta cikin wani hali da take bukatar wani bangare na dukiyar tsohon mijin nata domin samun damar taimaka wa rayuwa, la’akari da cewa itama tana da tata dukiyar, amma abin mamakin shine yadda ta nemi a bata rabin dukiyar dan wasan.

Al'umma da dama daga sassan duniya, na jinjina wa dan wasan, musamman yadda ya nuna kauna ga mahaifiyarsa, da kuma kaucewa fada wa irin wannan sarkakiya, la'akari da yadda matan 'yan kwallo da dama kan nemi makudan kudade idan suka nemi rabuwa da su.

Sai dai a wasu wuraren kuma, dan wasan ya sha suka, inda wasu ke ganin bai kamata ya mika ragamar dukiyar tasa kacokan ga asusun mahaifiyar tasa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.