Isa ga babban shafi

Yadda jadawalin wasannin da suka rage a gasar Zakarun Turai zai kasance

Chelsea, Bayern Munich, AC Milan da Benfica sun samu tabbacin kai wa gurbin ‘yan takwas a matakin daf da na kusa da karshe na gasar cin kofin zakarun Turai.

Tambarin hukumar shirya gasar zakarun Turai ta UEFA kenan
Tambarin hukumar shirya gasar zakarun Turai ta UEFA kenan © AFP
Talla

Manchester City, Liverpool da Real Madrid mai rike da kambun gasar kuwa har yanzu suna fatan zuwa zagayen ‘yan takwas din; A ranar Juma'a ne dai za a fitar da jadawalin dab da na kusa da na karshe a gasar.

Chelsea ce kadai a kungiyoyin Ingila da ta kai zagayen na kwata final bayan ta doke Borussia Dortmund da ci 2-1 a zagayen na ‘yan 16.

'Yan wasan Chelsea kenan yayinn fafata wa a Premier Ingila
'Yan wasan Chelsea kenan yayinn fafata wa a Premier Ingila POOL/AFP

Manchester City da Liverpool su ne sauran kungiyoyin gasar Premier da har yanzu za su iya kaiwa matakin ko kuma akasin haka, inda kungiyoyin biyu suka buga wasansu na biyu a wannan makon.

A ranar Talata ne City za ta kara da RB Leipzig a filin wasa na Etihad bayan da kungiyar karkashin Pep Guardiola ta tashi kunnen doki 1-1 a Jamus a wasan farko.

Ita kuwa Liverpool, za ta fuskanci wani gagarumin aiki ne a yunkurinta na kawar da rashin nasarar da tayi a hannun Real Madrid da ci 5-2 a zagayen farko, inda za a yi wasa na biyu ranar Laraba a Bernabeu.

Dan wasan Real Madrid Karim Benzema kenan daga hagu, tare da dan wasan Liverpool Trent Alexander-Arnold a wasan karshe na gasar Zakarun Turai, ranar 28 ga watan Mayun 2022.
Dan wasan Real Madrid Karim Benzema kenan daga hagu, tare da dan wasan Liverpool Trent Alexander-Arnold a wasan karshe na gasar Zakarun Turai, ranar 28 ga watan Mayun 2022. AFP - ANNE-CHRISTINE POUJOULAT

Dama Tottenham tuni aka yi waje da ita, bayan kayen da ta sha a zagayen farko a hannun AC Milan da ci 1-0 a zagayen farko, inda a zagaye na biyu kuma suka tashi a wasan nasu babu ci.

Bayern Munich da Benfica su ma sun tsallaka kasan zuwa matakin na gaba, inda Inter Milan ko Porto da Eintracht Frankfurt ko Napoli ke fatan haduwa da su a zagayen na ‘yan takwas ko kuma dab da na kusa da na karshe.

Jadawalin dab da na kusa da na karshe

Za a fitar da jadawalin kwata final da wasan kusa da na karshe a ranar 17 ga watan Maris, a birnin Nyon da ke Switzerland, wato shalkwatar UEFA.

Za a buga zagayen farko na kwata final ranar Talata, da Laraba, wato 11 da 12 ga Afrilu, sannan zagaye na biyu kuma, za a fafata ne a ranar 18 da 19 ga watan na Afrilu.

Yaushe ne za a buga wasan kusa da na karshe?

Zagayen farko na wasan kusa da na karshe za a yi shi ne ranar 9 da 10, ga watan Mayu, sai kuma ranar 16 da 17 ga watan Mayu da za a buga zagaye na biyu.

Ranar da za a buga wasan karshe

Wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai za a fafata shi ne a ranar 10 ga watan Yuni, a filin wasa na Ataturk Olympic  da ke birnin Istanbul, na kasar Turkiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.