Mai Liverpool ya ce kungiyarsa ba ta sayarwa ba ce
Mai kungiyar Liverpool John Henry ya musanta cewar yana shirin sayar da kungiyar, duk da cewa a shekarar da ta gabata ya nemi taimakon masu zuba hannun jari don sake karfafa Club din nasa.
Wallafawa ranar:
A cikin watan Nuwamban da ya gabata shugaban na Liverpool ya bayyana aniyar neman karin masu sayen hannayen jarin kungiyar, matakin da ya ce ko shakkah babu zai taimakawa kungiyar.
Idan za a iya tunawa shekaru 13 baya, kamfanin 'Fenway Sports Group' na John Henry, ya lale tsabar kudi fam miliyan 300 ya sayi Liverpool daga hadin gwiwar attijaran Amurka Tom Hicks da George Gillet.
A karkashin sabon shugabancin ne kuma Liverpool ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai a 2019, da kuma kofin gasar Firimiya a shekarar 2020, na farko da ta ci bayan shekaru 30.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu