Isa ga babban shafi

Gawar Christian Atsu ta isa Ghana

Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta sanar da cewa, dauko gawar tsohon dan wasan kwallon kafar kasar Christian Atsu wanda ya mutu a mummunar girgizar kasa da ta afku a kasar Turkiyya.

Christian Atsu
Christian Atsu © AFP - PAUL ELLIS
Talla

Atsu, mai shekaru 31, ya yi rashin sa’ar tsintar kansa cikin wadanda girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta rutsa da su a kasashen Turkiyya da Syria a ranar 6 ga watan Fabrairu, inda kawo yanzu aka tabbatar da cewar ta kashe mutane fiye da 46,500 a kasashen biyu.

Da farko dai an bayar da rahoton cewa an ceto tsohon dan wasan na Chelsea da Newcastle da ransa daga karkashin baraguzan ginin da suka rufta kwana guda bayan girgizar kasar, amma tun a lokacin ba a tabbatar da inda aka kaishi domin jinya ba, wanda kuma daga bisani labara ya sauya inda aka gano gawarsa a ranar Asabar da ta gabata.

Ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta ce babban yayan Atsu da abokiyar tagwaitakarsa suna tsaye a wurin da ake dauko gawarsa daga karkashin baraguzan gini a Turkiya.

Marigayin dai ya zura kwallo ta 33 kuma ta karshe a dukkanin wasannin da ya bugawa kungiyarsa ta Hatayspor a gasar Super Lig ta Turkiyya a ranar 5 ga watan Fabrairu, sa'o'i kadan kafin girgizar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.