Isa ga babban shafi

An tsinci gawar dan kwallon Ghana Atsu bayan girgizar kasar Turkiya

Majiyoyi a kasar Turkiya sun bayyana cewa an tsinci gawar dan kwallon Ghana Christian Atsu na kungiyar Hatayspor ta Turkiya a karkashin baraguzan gininsa da ke Hatay a kudancin kasar Turkiya.

Christian Atsu dan wasan Ghana da ya rasu a Turkiya
Christian Atsu dan wasan Ghana da ya rasu a Turkiya AP - Khalil Hamra
Talla

An gano gawar Atsu a karkashin baraguzan ginin, ana ci gaba da kwashe kayansa, an kuma gano wayarsa," in ji wakilinsa Murat Uzunmehmet.

Kafofin yada labaran Turkiya sun ce tsohon dan wasan Chelsea da Newcastle na Ingila mai shekaru 31 a duniya yana karkashin baraguzan gidan Rönesans,wata hasumiya mai hawa 12 da ta ruguje a girgizar kasar.

Da farko dai ofishin jakadancin Ghana da ke Turkiya da hukumar kwallon Ghana sun yi ikirarin cewa an gano dan wasan a raye, amma daga baya aka tabbatar da cewa wannan labarin karya ne.

Mutumen da  ya gina gidan , inda ake kyautata zaton an binne mutane 800, an kama shi a makon da ya gabata a lokacin da yake kokarin barin Turkiya.

Dan wasan Ghana Christian Atsu
Dan wasan Ghana Christian Atsu Justin TALLIS / AFP

Atsu ya koma kulob din Hatayspor na Turkiya a watan Satumba, wanda ke lardin Hatay (kudu), kusa da cibiyar girgizar kasa da ta afku a Turkiya a ranar 6 ga Fabrairu.

An samu asarar rayuka da dama biyo bayan girgizar kasa mai karfin gaske, mutane sama da 40,000 a kasashen Turkiya da Syria suka mutu, mutane da dama ne suka jikkata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.