Isa ga babban shafi

Harry Kane na shirin kamo Shearer da Rooney a yawan kwallayen Firimiya

Bayan nasarar shi ta zura kwallon da ya basu damar doke Manchester City a karshen mako, Harry Kane ya zama dan wasan Tottenham mafi zura kwallo inda ya dara Jimmy Greaves da a baya ake kwatanta su.

Hatta allunan filin wasan sun rika fitar da rubuce rubucen taya murna ga Harry Kane.
Hatta allunan filin wasan sun rika fitar da rubuce rubucen taya murna ga Harry Kane. REUTERS - DAVID KLEIN
Talla

Yanzu haka dai Kaftin na Ingila na da jumullar kwallaye 267 da ya zurawa Tottenham a wasanni daban-daban inda a Firimiya kadai ya ke da kwallaye 200 wanda ke nuna ‘yan wasa irinsu Alan Shearer me kwallo 260 da Wayne Rooney me kwallo 208 kadai ke gabanshi a yawan kwallayen firimiya.

Bayan kwallon ta Kane a minti na 15 hatta allunan filin wasa masu amfani da lantarki anga yadda suke rika fitar da rubutun ‘‘muna tayaka murna Kane’’.

Dan wasan mai shekaru 29 a watan disamban 2011 ne ya zurawa Tottenham kwallon farko, wanda ke nuna ya samu wannan nasara ne a shekaru 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.