Isa ga babban shafi

Newcastle ta kai wasan karshe na Carabao karon farko cikin shekaru 24

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ta kama hanyar lashe kofin Carabao bayan doke Southampton da kwallaye 2 da 1 a wasansu na daren jiya talata, wanda ya nuna a jumulla gida da waje tawagar ta Eddie Howe ta yi nasara da kwallaye 3 da 1.

'Yan wasan Newcastle yayin murnar samun nasara.
'Yan wasan Newcastle yayin murnar samun nasara. © REUTERS/David Klein
Talla

Nasarar ta Newcastle ta bata damar tunkarar wasan karshe na cin kofin na Carabao wanda ya kubce daga hannun Liverpool.

Bayan wasan Manchester United da Nottingham Forest na yau laraba ne Newcastle za ta san da kungiyar da za ta doka wasan na karshe a Wembley, duk da cewa dai United ke jagoranci bayan nasara kan Nottingham a haduwarsu ta farko da kwallaye 3 da nema, wanda ke nuna abu ne mai matukar wuya ta yi rashin nasara a haduwar ta yau domin kuwa har sai an zura mata kwallaye 4 ba ko daya ne za ta iya ficewa daga gasar.

Newcastle wadda ke matsayin ta 3 a teburin firimiyar Ingila, tun bayan zuwan Eddie Howe ta ke ci gaba da samun tagomashi inda a yanzu haka ta ke fatan iya samun gurbi a gasar cin kofin zakarun Turai.

Nasarar ta jiya mai cike da tarihi ta nuna yadda Newcastle za ta sanya kafa a Wembley karon farko tun 1999, kuma idan har ta yi nasarar lashe kofin zai zama karon farko da ta dage kofin wata gasa tun 1976.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.