Isa ga babban shafi

Newcastle ta musanta rahoton yiwuwar karbar aron Ronaldo

Kocin Newcastle Eddie Howe ya ce babu kamshin gaskiya a rahoton da ke cewa akwai wani sashi cikin yarjejeniyar Cristiano Ronaldo da Al Nassr, da ke cewa yana da damar tafiya kungiyar Newcastle United a matsayin aro, idan ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turai.

Kocin Newcastle United Eddie Howe
Kocin Newcastle United Eddie Howe Action Images via Reuters - Lee Smith
Talla

A ranar Talata kungiyar Al Nassr ta gabatar da Ronaldo gaban magoya bayanta, bayan da suka kulla yarjejeniyar kimanin Yuro miliyan 200 a tsawon shekaru biyu, wato daga yanzu har zuwa watan Yunin shekarar 2025.

Dan wasan mai shekaru 37 ya rabu da Manchester United ne a watan Nuwamba, bayan da ya yi wata hira inda ya soki kocinsa Erik ten Hag da shugabannin kungiyar.

Sai dai wani rahoto da aka buga a kasar Spain cikin wannan makon ya bayyana cewar dan wasan da ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar ya fara tunanin yiwuwar komawa gasar Premier.

Rahoton ya ce a cikin yarjejeniyar da ya sa wa hannu, Ronaldo da damar bugawa Newcastle, wadda kashi 80 na hannun jarinta mallakin ‘yann kasar Saudiya ne.

To amma kocin kungiyar ta Newccatle Eddie Howe ya shaida wa Sky Sports cewa suna yi wa Cristiano fatan alheri a sha’aninsa, sai dai babu kamshin gaskiya a cikin rahoton zai buga musu wasa a matsayin aro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.