Isa ga babban shafi

Morocco ta samu gayyatar taka leda a karkashin gasar Copa America

Hukumar Shirya gasar cin kofin kasashen da ke kudancin Amurka ta mika takardar gayyata ga kasar Morocco domin halartar gasar da za’ayi ta shekara mai zuwa a kasar Amurka saboda bajintar da ‘yan wasanta suka nuna a gasar cin kofin duniyar da ya gudana bara a Qatar. 

Tawagar kwallon kafar Morocco da ta nuna bajinta a gasar cin kofin Duniyar da ta gudana a Qatar.
Tawagar kwallon kafar Morocco da ta nuna bajinta a gasar cin kofin Duniyar da ta gudana a Qatar. REUTERS - CARL RECINE
Talla

Wakilan hukumar sun amince da aikewa Morocco wannan takardar gayyatar ce saboda yadda kasar ta cirewa Afirka kitse a wuta a gasar cin kofin duniya wajen kaiwa matakin kusa da na karshe. 

Gasar ta  COPA America da za a yi a shekara mai zuwa ita ce karo na 48, kuma za’a gudanar wadad za a fara a watan Yuni zuwa Yuli. 

Morocco ce za ta zama kasar Afirka ta farko da zata shiga cikin gasar ta COPA America wadda akan gayyaci wata kasa daga wata nahiya lokaci zuwa lokaci domin fafatawa a matsayin bakuwa. 

Kasar Argentina ce mai rike da kofin gasar sakamakon nasarar da ta samu a gasar da ta gabata wadda aka gayyaci kasashen Qatar da Japan. 

Rahotanni sun ce da an shirya gudanar da gasar ce a Ecuador amma sai kasar ta bayar da uzurin cewa ba zata iya daukar nauyin gasar ba. 

Gasar COPA America na mataki irin na gasar cin kofin Afirka da ake yi a nahiyar Afirka kowanne shekaru 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.