Isa ga babban shafi

An sanya kungiyar kwallon kafa ta Everton a kasuwa

Kwanaki kadan bayan sallamar kocinsu Frank Lampard, mai kungiyar Everton, Farhad Moshiri ya sanya club din a kasuwa, inda ya ke neman akalla fam miliyan 500. 

Filin wasa na Goodison Park a Ingila.
Filin wasa na Goodison Park a Ingila. AFP/File
Talla

A halin yanzu dai Everton ta na matsayin ta biyun karshe ne a teburin gasar Firimiya Ingila, bayan da ta buga wasanni 10 ba tare da samun nasara ba. 

Jaridar The Guardian da ke Birtaniya, ta rawaito cewa attajirin Ba-Iraniye kuma dan Birtaniyar na shirin siyar da kungiyar ne sakamakon sukar da ya ke sha tare da sauran shugabannin club din daga magoya bayansu a makonnin baya-bayan nan. 

Ya zuwa yanzu masu aniyar sayen kungiyar da dama sun gabatar da bukatarsu su, koda ya ke ba a kai ga bayyana daidaikunsu ba. 

A halin da ake ciki kuma, wasu taurarin ‘yan wasa na kungiyar ta Everton, irin su Anthony Gordon da Amadou Onana sun tsallake zuwa atisaye a kokarinsu na  ficewa daga kungiyar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.