Isa ga babban shafi

Portugal ta kulla yarjejeniya da tsohon kocin Belgium

Portugal ta nada tsohon kocin Belgium Roberto Martinez a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasanta.

Tsohon kocin tawagar 'yan wasan kasar Belgium Roberto Martinez
Tsohon kocin tawagar 'yan wasan kasar Belgium Roberto Martinez AFP/File
Talla

Martinez, mai shekaru 49, ya maye gurbin Fernando Santos, wanda ya ajiye aikinsa bayan da Portugal ta sha kashi a hannun Morocco a wasan daf da na kusa da karshe na gasar cin kofin duniya. 

Martinez ya ajiye aikin horas da Belgium ne bayan fitar da su daga gasar ta cin kofin duniya a Qatar a matakin rukuni, yana mai cewa ya yanke shawarar kawo karshen wa’adinsa na shekaru shida ne tun a shekarun baya, dan haka da ma zai rabu da aikin, ko da kuwa tawagar ta sa ta zama zakara.

Sai da kasar Belgium ta zama ta 1 a duniya wajen iya kwallon kafa a karkashin jagorancin Roberto Mertinez, bayan da a suka kare gasar cin kofin duniya da ta gudana a Rasha cikin shekarar 2018 a matsayi na uku.

Tuni dai sabon kocin dan kasar Spain ya bayyana cewar zai tattauna da Cristiano Ronaldo kan makomarsa a tawagar kwallon kafar Portugal, daya daga cikin batutuwan da aka zura idanu ana dakon ganin yadda zai tunkara.

Bayan da aka tambaye shi ko zai cigaba da gayyatar Ronaldo domin wakiltar Portugal, sai Martinez yace yana yanke shawara kan kwallon kafa ne a filin wasa ba a cikin  ofis ba. Dan haka zai fara ne da ganawa da dukkanin ‘yan wasan Portugal 26  da suka halarci  gasar cin kofin duniya a Qatar wanda kuma Cristiano na cikinsu.

Sabon kocin ya kara da cewar, Ronaldo ya shafe shekaru  19 yana cikin tawagar Portugal kuma ya cancanci a girmama shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.