Isa ga babban shafi

Liverpool ta fara tattauna don sayen Chukwueze dan Najeriya daga Villarreal

Liverpool ta fara shirin kulla yarjejeniya da dan wasan Najeriya, Samuel Chukwueze da ke kungiyar Villarreal.

Samuel Chukwueze dan wasan Najeriya dake kungiyar Villarreal a Spain.
Samuel Chukwueze dan wasan Najeriya dake kungiyar Villarreal a Spain. Getty Images
Talla

Kungiyar ta sake yunkurawa ne duk da cewar ta na da fitattun ‘yan wasan gaba, wanda kuma ba ta jima da kulla yarjejeniya da Cody Gakpo daga PSV Eindhoven ba.

Yanzu haka dai Gakpo ya shirya yin gwajin lafiyarsa da Liverpool yayin da kuma zai sanya alkalami a kan kwantiragin shekaru shida bayan ya bar PSV a kan fam miliyan 45.

A bangaren Samuel Chukwueze kuwa dama Liverpool din ta dade tana neman kullla yarjejeniya da shi, wanda a halin yanzu aka kiyasta darajarsa ta kusan €50m.

Chukwueze ya zura kwallaye biyar kuma ya taimaka wajen jefa shida a wasanni 23 da ya buga a kakar wasa ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.