Isa ga babban shafi

Juventus ta kira taron gaggawa bayan asarar yuro miliyan 239

Yau Talata masu hannayen jarin Juventus za su gana kan makomar kungiyar, wadda a cikin watan Nuwamban da ya gabata akasarin jami’an kungiyar suka yi murabus.

'Yan wasan kungiyar Juventus.
'Yan wasan kungiyar Juventus. © Reuters
Talla

Murabus din da baki dayan jami’an gudanarwar Juventus suka yi ya biyo bayan binciken da masu gabatar kara ke yi dangane da zarge-zargen da ake yi wa wasu 15 daga cikinsu na aikata almundahanar kuddade yayin ciniki da kuma bayar da da aron ‘yan wasa, gami da  sauran laifuka.

Ana sa ran taron manyan jami’an na Juventus su tattauna akan hasarar euro miliyan 239.3 da kungiyar ta tafka a kakar wasa ta 2021 da 2022 da ta kare.

Karo na biyar kenan a jere da Juventus ke tafka hasarar makudan kudaden shiga a duk shekara.

Tun da fari a ranar 23 ga watan Nuwamba aka shirya taron shugabannin na Juventus, amma aka yi ta jan kafa zuwa wannan Talata.

Shugaban Juventus Andrea Agnelli na daga cikin wadanda suka yi murabus, wanda ya kawo karshen jagorancinsa na shekaru 12 wanda ya kawo kofuna da dama sannan kuma ya sake kafa Juventus a matsayin daya daga cikin kungiyoyin da suka fi fice a Turai.

Sai dai a shekara ta 2021 nasarorin da kungiyar ke samu na lashe kofin Seria A suka zo karshe, yayin da kuma karsashinsu ya ragu a sauran manyan wasnnin Turai, bayan da suka kashe sama da Yuro miliyan 100 wajen sayen Cristiano Ronaldo daga Real Madrid shekaru uku da suka wuce.

Zuwan Ronaldo ya zo daidai da tasirin annobar corona wajen durkusar da tattalin arzikin duniya, matsalar da ta shafi fannin wasanni matuka, lamarin da ya  kara nauyin kudaden da kungiyar ke kashewa zuwa Yuro miliyan 700.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.