Isa ga babban shafi

Pogba ya tafi yana yaro ya kuma dawo a matsayin zakara - Juventus

Kungiyar Juventus ta bayyana murnar sake kulla yarjejeniya da Paul Pogba, wanda ya sake komawa kungiyar bayan rabuwa da Manchester United.

Paul Pogba bayan komawa tsohuwar kungiyarsa ta kungiyar Juventus daga Manchester United.
Paul Pogba bayan komawa tsohuwar kungiyarsa ta kungiyar Juventus daga Manchester United. AP
Talla

Dan wasan na kasar Faransa wanda ya lashe gasar cin kofin duniya, ya koma kungiyar Juventus dake gasar Seria A kyauta ne sakamakon karewar yarjejeniyarsa da United ba tare da ya sabunta ba.

Sanarwar da kungiyar ta wallafa a shafinta na yanar gizo a ranar Litinin ta ce, “ Paul ya dawo Turin, ya tafi yana yaro, ya kuma dawo a matsayin cikakken mutum, kuma zakara”

Pogba dai ya taka rawar gani yayin zamansa na Juventus a tsakanin shekarun 2012 zuwa 2016, kafin Manchester United ta saye shi akan Yuro miliyan 105 ciniki mafi tsada a waccan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.