Isa ga babban shafi

Eden Harzard ya ajiye bugawa kasarsa wasa

Kyaftin din tawagar kungiyar kwallon kafar Belgium Eden Harzard a hukumance ya bayyana murabus din sa daga yiwa kasar sa wasa bayan rashin abin azo a ganin da tawagar ta yi a gasar lashe kofin duniya da ke gudana a Qatar.

Dan wasan kasar Belgium Eden Hazard kenan
Dan wasan kasar Belgium Eden Hazard kenan © guardian
Talla

Harzard dai ya kawo karshen shekaru 14 da ya yi ya na bugawa Belgium wasa, ganin yadda ya samu koma baya wajen rawar da ya ke takawa a fagen tamula.

Tun bayan barin gasar Firimiyar Ingila da ya yi zuwa gasar Laliga, ya fara fuskantar naka su a salon wasan sa, kuma ba ta sauya zani ba a wakiltar Belguim da ya yi a gasar lashe kofin duniya.

A wani sako da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta, ya  mika godiyar sa gameda goyon bayan da ya samu a wasannin da ya yiwa kasar.

Tawagar ta Belgium dai ta fuskanci babbar koma baya a gasar lashe kofin duniya a wannan karon ta yadda ta gaza fitowa daga matakin rukuni, lamarin da ya sanya mai horas da ita Roberto Martinez aje aikin sa.

Hazard ya bugawa kasar ta Belgium wasanni 126 kuma ya ci mata kwallaye 33 tun bayan fara buga mata wasanni a shekarar 2008 ya na dan shekara 17.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.