Manchester United na sha'awar maye gurbin Ronaldo da Osimhen
Manchester United na nuna sha'awar sayen dan wasan Napoli Victor Osimhen a shekara mai zuwa amma ba ta shirya biyan farashin da kungiyar dake Seria A ta sanya a kansa ba, wanda a aka yi imanin ya kai Yuro miliyan 100 ko (£ 86m).
Wallafawa ranar:
Ficewar Ronaldo ya sa Man U ke bukatan dan wasan gaba, kuma ana tunanin kungiyar ta ciki gibin a watan Janairu, inda kocinta Erik Ten Hag ya damu kan zabin da ya kamata ya yi a zagaye na biyu na kakar.
Ana tunanin Osimhen na daya daga cikin ‘yan wasan da Kulub din suka dade suna harara.
Osimhen dan asalin Najeriya mai shekaru 23 ya zura kwallaye 38 kuma ya taimaka aka zura kwallaye 12 a wasanni 76 da ya buga wa Napoli tun lokacin da ya koma kungiyar ta Italiya daga Lille a watan Satumbar 2020.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu