Isa ga babban shafi

Rauni zai hana Sadio Mane na Senegal taka leda a gasar cin kofin Duniya

Dan wasan gaba na Senegale Sadio Mane da ke taka leda da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich a Jamus zai rasa damar haskawa a gasar cin kofin Duniya da ake shirin farawa ranar 20 ga watan da muke ciki na Nuwamba a Qatar saboda raunin da ya samu yayin wasan da kungiyarsa ta lallasa Werder Bremen da kwallaye 6 da 1.

Sadio Mané na Senegal da ke taka leda da Bayern Munich yayin wasansu da Leipzig.
Sadio Mané na Senegal da ke taka leda da Bayern Munich yayin wasansu da Leipzig. REUTERS - MATTHIAS RIETSCHEL
Talla

Tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci ne Mane ya samu rauni bayan taho mu gama da mai tsaron bayan Werder, Amos Pieper lamarin da ya tilasta fitar da shi daga fili tun gabanin karkare wasa.

Manajan Munich, Julian Nagelsmann ya ce bayan yiwa raunin na Mane hoto ya nuna cewa dan wasan na bukatar hutun makwanni gabanin sake taka leda, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da ya rage kwanaki 12 kasarsa Senegal ta doka wasanta na farko a gasar ta cin kofin Duniya.

Jaridar wasanni ta L’Equipe ta ruwaito hukumar kwallon kafar Senegal na cewa babu tabbacin tauraron na ta ya iya taka leda a gasar ta cin kofin Duniya.

Mane wanda shi ya ci kwallon da ta bai wa kasar damar samun tikitin zuwa gasar ta cin kofin Duniya yayin karawarsu da Masar, na sahun 'yan wasan Senegal da suka sauya fasalin tawagar ta yadda ta zama gagarabadau tsakanin takwarorinta na Afrika.

Halin rashin lafiyar ta Mane na nuna cewa zai rasa damar karawa da tsohon abokin wasansa a Liverpool wato Virgil van Dijk wanda kasashensu biyu Netherlands da Senegal ke shirin haduwa a wasan farko na rukunin A a gasar ta cin kofin Duniya.

Masu sharhi dai na ganin rashin Sadio Mane a tawagar ta Senegal zai zama babban nakasu ga Aliou Cisse wanda ya jagoranci kasar har zuwa matakin gab da na kusa da karshe a gasar cin kofin Duniya ta 2018, wadda ta zama tawagar Afrika daya tilo da ta kai matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.