Isa ga babban shafi

Australia ta caccaki Qatar kan cin zarafin baki gabanin gasar cin kofin Duniya

Babbar tawagar kwallon kafar Australia ta caccaki jerin cin zarafin bil adama a Qatar, gabanin gasar cin kofin duniya da ke tafe a watan Nuwamban wannan shekarar, lamarin da ya sa ta kasance tawaga ta farko da ke cikin wannan gasa da ta caccaki kasar da ke karbar bakuncin gasar.

Zarge-zarge sun dabaibaiye Qatar ne tun bayan da kasar ta samu damar karbar gasar ta cin kofin Duniya.
Zarge-zarge sun dabaibaiye Qatar ne tun bayan da kasar ta samu damar karbar gasar ta cin kofin Duniya. AP - Darko Bandic
Talla

Gasar cin kofin duniyar da za'a fara a ranar 20 ga watan Nuwamba ta fuskanci cece-kuce tun daga lokacin da aka bai wa Qatar damar karbar bakoncin shekaru 12 da suka wuce.

Hukumar kwallon kafar Australia ta ce ta san cewa an yi sauye-sauye ga dokokin Qatar ta yadda za su kare hakkokin ma’aikata, kana ta karfafawa masu ruwa da tsaki gwiwa su goyi bayan sauye-sauyen.

‘Yan wasan tawagar ta Australia sun ce sun samu labarin irin wahalhalun da ma’aikata bakin haure da iyalansu ke sha a Qatar.

Tun da farko a wannan mako, hukumomin Qatar suka caccaki abin da suka bayyana a matsayin munafurci daga wasu kasashen duniya a game da batun take hakkin dan adam a kasar gabanin gasar cin kofin duniya ta 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.