Isa ga babban shafi

EURO 2022: Ingila ta kafa tarihin farko na lashe gasar mata

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta samu nasarar lashe kofin mata na nahiyar Turai bayan da ta doke takwararta ta Jamus da ci 2 da 1.

Karon farko kenan da tawagar Ingila ta mata ta lashe gasar cin kofin nahiyar Turai ta EURO
Karon farko kenan da tawagar Ingila ta mata ta lashe gasar cin kofin nahiyar Turai ta EURO © 1xnews
Talla

Kafin fara wasan karshen da Ingala ta kara da tsohuwar abokiyar hamayyar ta Jamus da tasha kashi a hannunta a lokuta da dama, mai horas da tawagar ta Ingila Sarina Wiegman ta ce basa tsaron kowa.

Ana dai ganin tawagar ta Jamus a matsayin gagara tsara a gasar ta mata, domin sau 8 tana lashe gasar ta nahiyar Turai da kofin duniya sau biyu sannan kungiyoyin da ke wakiltar kasar sun lashe gasar zakarun Turai sau Tara adadin da ya zarce na kowacce kasa.

Toh sai dai a wannan karon reshe ne ya juye da mujiya, domin dai kwallon da Chloe Kelly ta jefa bayan karin lokaci ya baiwa tawagar nasarar lashe babbar gasa ta farko a tarihi a gaban ‘yan kallo sama da dubu 87 da ke cikin filin wasa na Wembley.

Irin wannan rawar gani da mai horaswa Wiegman tayi, irinta ta taba yi a shekarar 2017 lokacin da ta lashe gasar da tawagar mata ta Netherlands, sannan a shekarar 2019 ta kai tawagar kasarta wasan karshe na lashe kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.