Isa ga babban shafi

An saida tikitin kallon wasanni fiye da miliyan daya gabanin hallara a Qatar

Masu shirya gasar kwallon kafa ta duniya a Qatar sun ce kimanin tikiti kallon wasanni miliyan 1 da dubu 200 ne suka saida.

Tambarin gasar cin kofin duniya a daya daga cikin dogayen gine-ginen da suke Doha, babban birnin kasar Qatar.
Tambarin gasar cin kofin duniya a daya daga cikin dogayen gine-ginen da suke Doha, babban birnin kasar Qatar. © REUTERS/Naseem Zeitoun
Talla

Karo na farko kenan da ake bayyana adadin tikitin shiga filayen wasannin da aka yi cinikinsu, a yayin da ake tunkarar fara gasar ta cin kofin duniya daga watan Nuwamban da ke tafe zuwa Disamba.

Yayin sanar da alkaluman, babban jami'in shirya gasar Hassan Al-Thawadi ya ce yanzu haka akwai bukatun neman sayen tikitin kallon wasanni kusan miliyan 40.

Sai dai ya ce za a sayar da tikiti miliyan biyu ne gaba daya, inda za a kuma ware karin wasu miliyan daya ga hukumar FIFA da masu daukar nauyin gasar.

Domin takaita yawan magoya bayan da za su kwarar cikin Qatar, gwamnati ta ce, mutanen dake da tikitin wasa shiga kallon wasanni ne kawai za a baiwa damar shiga cikin kasar mai arzikin iskar gas, a yayin gudanar gasar cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.