Isa ga babban shafi

Chelsea ta tabbatar da sayen Raheem Sterling daga City

Chelsea ta tabbatar da daukar dan wasan gaban Ingila Raheem Sterling daga Manchester City kan kudi fan miliyan 50.

Chelsea ta tabbatar da daukar dan wasan gaban Ingila Raheem Sterling daga Manchester City kan kudi fan miliyan 50.
Chelsea ta tabbatar da daukar dan wasan gaban Ingila Raheem Sterling daga Manchester City kan kudi fan miliyan 50. © Chelsea
Talla

Sterling, mai shekara 27, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar a Stamford Bridge.

City ta sayi Sterling daga Liverpool kan kudi fam miliyan 49 a shekarar 2015. Ya ci kwallaye 131 a wasanni 339, inda ya lashe kofunan gasar Premier hudu.

Wasanni 77 ya bugawa Ingila, kuma Sterling shine babban dan wasa na farko da kocin Chelsea Thomas Tuchel ya dauko tun bayan da Todd Boehly ya karbi ragamar kungiyar.

Sterling ya ce "Tabbas na samu nasarori da yawa a rayuwata ya zuwa yanzu, amma akwai saura da yawa da zan iya cimma kuma ina matukar fatan yin hakan da jesin Chelsea, karkashin jagorancin Thomas."

"London gidana ne kuma inda abin ya faro ne a gare ni, kuma abin mamaki ne a yanzu ina samun damar yin wasa a gaban abokai da 'yan uwa a mako a mako a Stamford Bridge. Ina matukar fatan haduwa da magoya baya a can nan ba da jimawa ba. ."

A halin da ake ciki, Chelsea na shirin sayan dan wasan baya na Napoli Kalidou Koulibaly kuma tana dab da neman dan wasan bayan Manchester City Nathan Ake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.