Isa ga babban shafi

Raheem Sterling na gab da amincewa da tayin Chelsea

Dan wasan gaba na Manchester City Raheem Sterling ya amince da sharuddan da ke kunshe a tayin da Chelsea ta yi masa wanda ke nuna yiwuwar dan wasan ya koma Stamford Bridges a sabuwar kaka.

Da yiwuwar Raheem Sterling ya koma Chelsea da taka leda a kaka mai zuwa.
Da yiwuwar Raheem Sterling ya koma Chelsea da taka leda a kaka mai zuwa. POOL/AFP
Talla

Duk da cewa Sterling dan Ingila mai shkearu 27 na da sauran kwantiragin shekara guda tsakaninsa da Manchester City alamu na nuna kungiyar ba ta bukatar ci gaba da aiki da shi yayinda kungiyoyi daga ciki da wajen Ingila suka nuna bukatar sayenshi.

A shekarar 2015 ne City ta sayo Sterling daga Liverpool kan farashin yuro miliyan 49 inda zuwa yanzu ya zura kwallaye 131 cikin wasanni 339 a Etihad.

Idan har Chelsea da Sterling suka kai ga cimma jituwa kenan dan wasan wanda ya dokawa Ingila wasanni 77 zai zama na farko da Chelsea ta saya a kasuwar musayar ‘yan wasa don tunkarar sabuwar kaka.

Sauran kungiyoyin da ke harin Sterling sun kunshi Barcelona da Real Madrid da kuma Bayern Munich sai dai a cewarsa yafi gamsuwa da tayin Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.