Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Chiellini zai raba gari da Juventus gabanin rataye takalmansa

Mai tsaron baya na Italiya Giorgio Chiellini ya tabbatar da jita-jitar shirin raba garinsa da Juventus a karshen wannan kaka bayan shafe shekaru 17 ya na taka leda da kungiyar.

Mai tsaron baya na Juventus Giorgio Chiellini.
Mai tsaron baya na Juventus Giorgio Chiellini. Reuters / Giorgio Perottino Livepic
Talla

Chiellini wanda ke sanar da matakin bayan rashin nasarar Juventus hannun Inter Milan da kwallaye 2 da 4 a wasan karshe na cin kofin Coppa Italia a daren jiya laraba, ya ce ya yi iyakar abin da zai iya, yanzu kuma lokaci ne daya kamata ya ja da baya.

A zantawarsa da manema labarai bayan wasan na jiya Chiellini wanda ya kai Italy ga nasarar dage kofin Euro bayan doke Ingila a bara, ya ce ya bayar da gagarumar gudunmawa a shekaru 10 da suka gabata, yanzu kuma ya ragewa saura su dora daga inda ya tsaya. 

Dan wasan ya bayyana cewa ko shakka babu zai yi ban kwana da magoya bayansa da ke filin wasan Juventus a litinin din nan bayan wasansu da Lazio gabanin tattakinsu zuwa Fiorentina a ranar 22 ga watan nan da zai zama wasan karshe na wannan kaka.

Tun bayan komawarsa Juventus daga Fiorentina a shekarar 2005, Chiellini mai shekaru 37 ya yi nasarar daga kofunan Serie A 9 da Coppa Italia 5.

Tun tuni dama dan wasan ya sanar da shirin rataye takalmansa bayan haduwar Italy da Argentina cikin watan yuni a Wembely karkashin gasar zakarun nahiyoyi da aka dawo da ita.

Juventus dai na shirin kammala kakar bana ne a sahun 'yan hudun saman teburi wanda ke nuna cewa za ta samu sukunin taka leda a gasar cin kofin zakarun Turai ta badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.