Isa ga babban shafi
SAUYA-SHEKA

Ba zan sake yiwa Juventus wasa ba - Ronaldo

Mai Horar da ‘Yan wasan kungiyar Juventus Massimiliano Allegri yace Cristiano Ronaldo ya shaida masa cewar ba zai sake yiwa kungiyar wasa ba, yayin da ake ci gaba da rade radin cewar zai koma kungiyar Manchester City.

Dan wasan gaba na Juventus Cristiano Ronaldo
Dan wasan gaba na Juventus Cristiano Ronaldo Marco BERTORELLO AFP/File
Talla

Allegri ya shaidawa manema labarai cewar yayin tattaunawar su da tauraron ‘dan wasan jiya, Ronaldo ya shaida masa cewar baya fatar ci gaba da zama a  Juventus saboda haka ba’a sanya shi cikin ‘Yan wasan da za su yiwa kungiyar wasa gobe ba.

Mai horar da ‘yan wasan yace wannan ne dalilin da ya sa yau juma’a Ronaldo bai fita atisaye tare da sauran ‘yan wasan kungiyar ba kamar yadda aka saba.

Rahotanni sun ce yanzu haka Manchester United da Manchester City na rige rigen daukar Cristiano Ronaldo
Rahotanni sun ce yanzu haka Manchester United da Manchester City na rige rigen daukar Cristiano Ronaldo MIGUEL MEDINA AFP/File

Allegri ya bayyana bacin ran sa da ‘dan wasan saboda matakin da ya dauka, yayin da yake cewa haka rayuwa take, lura da irin zaratan ‘yan wasan da suka yiwa Juventus wasa a baya, irin su Sivori da Platini da Del Piero da Zidane da Buffon wadanda yanzu haka duk sun zama tarihi.

Manajan yace Ronaldo ya zauna da su na shekaru 3, ya kuma bada gudumawar sa, saboda haka rayuwa zata ci gaba ko bayan tafiyar sa.

Yanzu haka rahotanni sun bayyana cewar kungiyar Manchester United ta bi sahun Manchester City wajen neman daukar Ronaldo wanda yake da sauran kwangilar shekara guda da kungiyar ta Juventus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.