Isa ga babban shafi
Wasanni

Manchester City tayi watsi da tayin sayen Ronaldo

Makomar Cristiano Ronaldo a fagen kwallo na ci gaba da kasancewa cikin yanayi na rashin tabbas, bayan da zakarun gasar Firimiya Lig Manchester City, suka yi watsi da tayin kulla yarjejeniya da shi daga Juventus a wannan bazarar.

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. MARCO BERTORELLO AFP/Archivos
Talla

Kodayake tsohon tauraron na Real Madrid ya musanta tuntubar City cikin wata sanarwa a makon da ya gabata, rahotanni daga kafafe da dama a Turai sun nanata cewa yanzu haka Ronaldo yana matsa lamba don rabuwa ga Juventus kafin karewar lokacin hada-hadar sauyin shekar ‘yan wasa a wannan bazara, kamar yadda fitacciyar Jaridar wasanni ta L'Equipe da ke faransa ta ruwaito

Jorge Mendes wakilin fitattun 'yan wasan kwallon kafa a duniya.
Jorge Mendes wakilin fitattun 'yan wasan kwallon kafa a duniya. AFP/Archives

Rahotanni sun ce a halin da ake ciki, wakilin Ronaldo, Jorge Mendes, yana birnin Manchester kasancewar yana wakiltar dan wasan City, Bernardo Silva, wanda ke neman barin kungiyar a cikin bazarar nan.

A cewar jaridar L’Equipe Mendes yana ƙoƙarin kulla yarjejeniyar musaya da za ta kai ga Silva ya koma Juventus, Ronaldo kuma ya koma City.

Sai dai ga dukkanin alamu City ba ta son sanya Ronaldo zama daya daga cikin masu samun albashi mai tsoka a kungiyar ganin yawan albashin sa a Juventus.

Har yanzu Manchester City ta mai da hankali ne kan siyan kaftin din Ingila, Harry Kane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.