Isa ga babban shafi
Gasar Zakarun Turai

Dan Najeriya ya taimakawa Villareal zuwa wasan daf da na karshe na zakarun Turai

Villareal ta kai karawar daf da karshe na gasar cin kofin zakarun turai, bayan tashi wasa 1-1 a gidan Bayern Munich daren Laraba

Dan wasan Bayern Munich Thomas Muller bayan rasa damar jefa kwallo a ragar kungiyar Villareal
Dan wasan Bayern Munich Thomas Muller bayan rasa damar jefa kwallo a ragar kungiyar Villareal © Photo by Chris Brunskill/Fantasista/Getty Images
Talla

Kwallan da dan wasan Najeriya Samuel Chukwueze ya farke a minmtuna na 88 ya taimakawa kungiyar ta Spain zuwa zagayen daf da karshe a gasar, saboda wasan farko da aka fafata ranar 6 ga watan Afirilu Villareal ta ci Bayern Munich 1- 0 a gida.

Robert Lewandowski ne ya fara ci wa Bayern kwallo, a mintuna na 52 wato bayan dawowa daga hutun rabin lokacin a Allianz Arena, amma kuma farkewar da Chukwueze yayi ya dagulawa Bayern lissafi.

Yanzu dai  Villareal na jiran duk wadda ta yi nasara tsakanin Liverpool da Benfica da za su kece raini ranar Laraba.

A wasan farko da kungiyoyin suka fafata ranar Talata 5 ga watan Afirilu, Liverpool ta doke Benfica 3-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.