Madrid na shirin karbar bakuncin Chelsea a gasar Turai
Yau za’a fafata tsakanin kungiyar Real Madrid da Chelsea a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, inda ake saran kungiya daya daga cikin su ta samu damar wucewa zuwa zagaye na gaba.
Wallafawa ranar:
A karawar da akayi makon jiya, Madrid ta doke Chelsea mai rike da kofin gasar da ci 3-1 a wasan da ya gudana a Ingila wanda Karim Benzema ya jefa kwallayen guda 3 shi kadai.
Wannan ya sa ake kallon karawar ta yau a matsayin mai matukar muhimmanci ga kungiyoyin guda 2, kuma dole daya daga cikin su ta fice daren yau.
Rahotanni sun ce Chelsea wadda ta lallasa Southampton da ci 6-0 a gasar Firimiya ba zata samu damar amfani da yan wasan ta irin su Romelu Lukaku da Callum Hudson-Odoi da Ben Chilwell ba saboda raunukan da suka fama da shi.
Mai horar da Yan wasan Madrid Carlo Ancelotti yace har yanzu da sauran aiki a gaban su kafin samun tikitin wasan kusa da na karshe a karawar yammacin yau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu