Isa ga babban shafi
Gasar Zakarun Turai

Kocin PSG ya caccaki alkalan wasan da suka fafata da Real Madrid

Kocin PSG Mauricio Pochettino ya caccaki tawagar jami’an da suka yi alkalancin karawarsu da Real Madrid a gasar Zakarun Turai zagaye na biyu inda ya tambayi dalilin da yasa ba a yi amfani da na’urar VAR ba wajen soke kwallon farko da Real Madrid ta ci, wadda ta bude kofar fitar da kungiyarsa daga gasar zakarun Turai a ranar Laraba.

Mai horas da kungiyar PSG Mauricio Pochettino.
Mai horas da kungiyar PSG Mauricio Pochettino. © REUTERS/Piroschka Van De Wouw
Talla

A cewar Pochettino, abin kunya ne, ganin yadda Real Madrid ba ta samu nasarar jefa kwallon farko ba, sai da Benzema yayi wa mai tsaron ragarsu Donnarumma keta, alkalan wasa kuma nag ani suka yi biris da abinda ya faru.

Da fari dai zakarun na gasar Ligue 1 sun sa ran tsallakawa zuwa zagayen kwata finals bayan da Kylian Mbappe ya jefa kwallo ta biyu a ragar Madrid, amma daga bisani Benzema ya jefa musu kwallaye 3, aka tashi wasa 3-2.

Kayen da PSG ta sha a daren ranar Laraba ya sanya adadin ficewar ta daga gasar Zakarun Turai a zagayen 'siri daya kwale' kaiwa sau hudu bayan da suka samu nasarar a zagayen farko na karawar da suka yi a zagayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.