Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Rauni zai hana Kante taka leda a wasan Chelsea da Juventus

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta ce dan wasan ta na tsakiya N’Golo Kante ba zai samu damar taka leda a karawarsu da Juventus yau laraba karkashin gasar cin kofin zakarun Turai ba.

N'Golo Kante tare da mai horarwa na Chelsea Thomas Tuchel.
N'Golo Kante tare da mai horarwa na Chelsea Thomas Tuchel. Adrian DENNIS POOL/AFP/File
Talla

Mai horar da kungiyar Thomas Tuchel da ke tabbatar da rashin Kante a tawagar tasa ta yau, ya ce dan wasan na Faransa da ya dage kofin duniya zai rasa karawar ne sakamakon harbuwa da cutar coronavirus.

Kocin na Chelsea mai rike da kambun gasar ta zakarun Turai, ya ce tawagarsa za ta yi tattaki zuwa Turin ba tare da dan wasan na tsakiya mai shekaru 30 ba.

Tuchel ya ce baya ga Kante da zai rasa karawar akwai kuma ‘yan wasa irinsu Christian Pulisic da Mason Mount da kuma Reece James wadanda dukkaninsu ba za su bi tawagar zuwa Italiya ba, saboda raunin da suka samu yayin wasansu da Manchester City a karshen mako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.