Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

FIFA ta ladabtar da Hungary kan nuna wariya a wasansu da Ingila

Hukumar FIFA ta haramtawa Hungary baiwa magoya bayanta damar shiga kallon wasanninta har guda 2 a jere, matakin da ke matsayin hukuncin wariyar da ‘yan wasan Ingila suka fuskanta a kasar yayin wasannin neman gurbi a gasar cin kofin duniya tsakanin kasashen biyu ranar 2 ga watan Satumba.

Tambarin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.
Tambarin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA. AP - Alessandro Della Bella
Talla

Sanarwar FIFA da ke cin tarar hukumar kwallon kafar ta Hungary yuro dubu 158 ta kuma bayyana cewa hukumar baza ta lamunci kowanne nau’in nuna wariya a kwallo ba.

Ita kanta Uefa ta yiwa hukumar kwallon kafar ta Hungary makamancin hukuncin ta hanyar cin tarar ta yuro dubu 85 da kuma hana ‘yan kallo shiga fili a wasanni 3 duk dai dangane da nuna wariyar amma wannan yayin wasannin Euro 2020 da suka gudana cikin watan yuni zuwa Yuli.

‘Yan wasan da suka gamu da nuna wariyar sun hada da Raheem Sterling da kuma Jude Bellingham wadanda magoya baya suka riga jifa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci yayin wasan kasashen biyu a Puskas Arena wanda Ingilar ta yi nasara kan Hungary da kwallo 3 da nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.