Isa ga babban shafi
Wasanni - Ingila

Greelish na gaf da zama dan wasa mafi tsada a Birtaniya

Manchester City na gaf da sayen dan wasan Aston Villa Jack Grealish kan fam miliyan 100, yarjejeniyar da idsan ta tabbata za ta sanya dan wasan mai shekaru 25 kafa tarihin zama mafi tsada a Birtaniya.

Fitaccen dan wasan Aston Villa Jack Grealish.
Fitaccen dan wasan Aston Villa Jack Grealish. © Getty Images
Talla

Farashin da City ke shirin biya kan Greelish dai ya zarce fam miliyan 89 da Manchester United ta biya don sake sayo dan wasan Faransa Paul Pogba daga Juventus a shekarar 2016.

Bayanai sun ce idan aka kammala kulla yarjejeniya kan lokaci dan wasan na Ingila zai samu damar bugawa Manchester City wasan Community Shield da za ta kara da Leicester City ranar Asabar.

A watan Satumban shekarar bara Grealish ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar shekaru biyar tare da Aston Villa.

Kocin City Pep Guardiola ya bayyana kwarin gwiwar cewa kwarewar Grealish za ta karawa tawagarsa karfin maciya kwallo da ake ganin kungiyarsa ta mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.