Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

Real Madrid ta baiwa Varane damar fara tattaunawa da United

Kungiyar Real Madrid ta baiwa dan wasanta mai tsaron baya Rafael Varane damar fara tattaunawa da Manchester United kan yiwuwar kulla yarjejeniya da ita.

Rafael Varane.
Rafael Varane. AFP/Archives
Talla

Fitacciyar jaridar wasanni ta Marca dake kasar Spain ta ruwaito cewar Real Madrid ta cimma matsayar kin tsawaita yarjejeniyar ta da Varane wadda za ta kare a karashen sabuwar kakar wasan da za a shiga.

Bayanai sun ce a shirye kungiyar Real Madrid take ta amince da karbar euro miliyan 50 kan dan wasan nata mai shekaru 28, wanda aka dade ana alakanta shi da komawa taka leda a Manchester United.

Jadon Sancho ne fitaccen dan wasa na baya bayan da United ta kulla yarjejeniya da shi daga Borussia Dortmund kan euro miliyan 73, a yanzu kuma take fatan karfafa tsaron bayanta da Varane idan ciniki ya tabbata tsakaninta da Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.