Isa ga babban shafi
Wasanni

Euro 2020 - An kama mutane 11 da suka ci zarafin 'yan wasan Ingila

'Yan sandan Birtaniya sun cafke mutane 11 a ci gaba da binciken da suke domin zakulo wadanda suka aikata laifin cin zarafin wasu ‘yan wasan Ingila ta hanyar furta musu kalaman nun wariyar launi a sakwannin da suka wallafa ta kafofin sada zumunta, bayan wasan karshe na gasar Euro 2020.

'Yan wasan Ingila, Marcus Rashford, Jadon Sancho, Bukayo Sakaa da Harry Kane
'Yan wasan Ingila, Marcus Rashford, Jadon Sancho, Bukayo Sakaa da Harry Kane © Sky Sports
Talla

‘Yan wasan da aka cin zarafin nasu dai sun hada da Marcus Rashford, Jadon Sancho da Bukayo Sakaa.

Sashin 'Yan Sanda dake lura da wasannin Kwallon Kafa na Birtaniya ya sanar da tattara rahotanni akalla 600, tare da tantance 207 a matsayina laifukan cin zarafi na kalaman wariyar launin fata da aka aika wa' yan wasan Ingila bakar fata bayan gaza lashe Euro 2020 da suka yi.

Daga cikin jerin sakwannin da aka tantance, 123 an wallafa su ne daga kasashen ketare, a yayin da aka wallafa 34 a cikin Birtaniya.

Cin zarafin da aka yiwa Marcus Rashford, Jadon Sancho da Bukayo Sakaa ta kafofin sada zumunta bayan barar da damarmakinsua na bugun fanereti, ya haifar da yin Allah-wadai daga hukumar kwallon kafa ta Ingila, kocin kasar Gareth Southgate da kuma Firaministan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.