Isa ga babban shafi
Wasanni - Ingila

Kungiyar Everton ta kulla yarjejeniya da Benitez

Kungiyar Everton ta kulla yarjejeniyar shekaru 3 da tsohon kocin Liverpool da Newcastle United Rafael Benitez.

Sabon kocin Everton Rafael Benitez.
Sabon kocin Everton Rafael Benitez. Action Images via Reuters - LEE SMITH
Talla

Everton dai ta share makwanni ta na laluben wanda zai maye gurbin tsohon kocinta Carlo Ancelotti da ya koma tsohuwar kungiyarsa Real Madrid, inda kafin cimma daukar Benitez, ta tattaunaw da tsohon kungiyar Wolves Nuno Espirito.

Rafael Benitez ya horas da Liverpool a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2010 inda tare da su ya lashe kofin gasar zakarun Turai 1 da kuma kofin FA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.