Isa ga babban shafi
Wasanni

Mbappe zai ci gaba da zama a PSG - Al-Khelaifi

Shugaban kungiyar Paris Saint - Germain na kasar Faransa Nasser Al-Khelaifi ya kawo karshen duk wasu zantuka dake alakanta batun sayar da gwarzon dan wasan gaba na kungiyar Kylian Mbappe.

Dan wasan PSG Kylian Mbappe yayin murnar zuru kwallo a wasan karshe da suka kara da Monaco ranar 9 ga watan Mayu 2021.
Dan wasan PSG Kylian Mbappe yayin murnar zuru kwallo a wasan karshe da suka kara da Monaco ranar 9 ga watan Mayu 2021. FRANCK FIFE AFP
Talla

Da yake shaidawa jaridar L’Equipe, Al-Khalifi yace, Mbappe zai ci gaba da kasancewa daram a babban birnin Faransa wata Paris, yana mai cewa, basu da niyyar sayar da Mbappe, hasalima dan wasan bazai koma ko ‘ina a kyauta ba.

Dan wasan París Saint-Germain Kylian Mbappe lokacin sarrafa tamola yayin wasa  ranar 28 ga watan Afrilu 2021
Dan wasan París Saint-Germain Kylian Mbappe lokacin sarrafa tamola yayin wasa ranar 28 ga watan Afrilu 2021 Anne-Christine POUJOULAT AFP

A watan Yuni shekarar 2022 ya kamata kwantiragin Mbappe ya kare, kuma ansha alankata shi da komawa kungiyar Real Madrid dake Spain.

Barcelona bata kudin sayen Neymar 

Shugaban na PSG yayi kuma tsokaci dangane da batun komawar Neymar Junior zuwa Barcelona, inda yace kungiyar ta Katolonia bata da kudin sayen dan wasan a yanzu, hasalima dan wasan bashi da niyyar yiwa tsohowar kungiyarsa kome.

Dan wasan PSG Neymar Junior
Dan wasan PSG Neymar Junior REUTERS - STEPHANE MAHE

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.