Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Henry Thierry ya koma horar da kungiyar kasar Belgium

Hukumar kwallon kafar Belgium ta gayyaci tsohon mataimakin manajan kwallon kafar kasar Henry Thierry domin komawa matsayin sa don aiki tare da Roberto Martinez a daidai lokacin da ake shirin fara gasar cin kofin Turai ranar 11 ga watan gobe.

Thierry Henry mataimakin mai horas da tawagar kwallon kafa ta kasar Belgium.
Thierry Henry mataimakin mai horas da tawagar kwallon kafa ta kasar Belgium. Sebastien ST-JEAN AFP/Archives
Talla

Hukumomin kasar sun ce suna maraba da dawowar Henry wanda ya taba aiki da Martinez lokacin da ya jagoranci kasar tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018.

Shima tsohon tauraron kasar Faransa da ya yiwa kungiyar Monaco da Arsenal da kuma Barcelona wasa ya tabbatar da labarin a shafin sa na Facebook.

Wannan labari da kafofin yada labaran kasar suka ruwaito ya baiwa mutanen Belgium da dama mamaki ganin cewar an dauki lokaci tsakanin Henry da kungiyar.

Henry ya taka rawa sosai wajen aiki akan yan wasan gaba na Belgium irin su Romelu Lukaku da Mitchy Batshuayi da Christian Benteke abinda ya taimaka musu damar zuwa wasan kusa da na karshe na cin kofin duniya na shekarar 2018.

Kafin dai wannan lokaci, Henry bashi da aiki tun bayan aje mukamin sa na manaja a kungiyarkwallon kafar Montreal dake Amurka rabar 25 ga watan Fabarairun bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.