Isa ga babban shafi
Wasanni - Ingila

West Brom ta fice daga Firimiya, City na dakon nasarar lashe kofin bana

Kungiyar West Brom ta fice daga ajin kwararru na gasar Firimiyar Ingila inda a yanzu ta koma matakin gasar kwallon kafa ta biyu, bayan da a jiya Lahadi Arsenal ta lallasa ta da kwallaye 3-1.

'Yan wasan Arsenal yayin murnar lallasa kungiyar West Brom da kwallaye 3-1 a gasar Firimiyar Ingila. 09/05/2021.
'Yan wasan Arsenal yayin murnar lallasa kungiyar West Brom da kwallaye 3-1 a gasar Firimiyar Ingila. 09/05/2021. © Pool via REUTERS/Andy Rain
Talla

Arsenal ta samu nasarar ce ta hannun ‘yan wasanta Emile Smith, Nicolas Pepe, da kuma Willian, yayin da Matheus Pereira ya ciwa West Brom kwallon ta tilo.

Yayin da ake shirin karkare kakar wasa ta bana a gasar ta Firimiya, yanzu haka Arsenal tana mataki na 9 da maki 52, yayin da West Brom da ta yi waje daga gasar ke da maki 26 a matsayin ta 19.

Dan wasan Manchester City Benjamin Mendy yayin karafkiya da dan wasan Chelsea Timo Werner yayin fafatawarsu a gasar Firimiya. 08/05/2021
Dan wasan Manchester City Benjamin Mendy yayin karafkiya da dan wasan Chelsea Timo Werner yayin fafatawarsu a gasar Firimiya. 08/05/2021 © Pool via REUTERS/Adam Davy

A dai gasar Firimiyar ta Ingila, har yanzu Manchester City dake kan gaba da maki 80 tazarar maki 10 tsakaninta da Manchester United na dakon kara buga wasau wasannin kafin nasarar lashe kofin gasar ta bana ya tabbata gare ta.

Wannan jira kuwa ya biyo bayan rashin nasarar da kungiyar ta Cityn tayi da 2-1 a wasan da suka kara da Chelsea a ranar Asabar, yayin da ita kuma Manchester United ta samu nasarar doke Aston Villa da 3-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.